Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohi 12 Ne Suka Dade Basu Biya Ma'aikatansu Ba


Alhaji Yahaya Bello gwamnan jihar Kogi, jihar da ta fi kowace jiha matsalar rashin biyan albashin ama'aikata
Alhaji Yahaya Bello gwamnan jihar Kogi, jihar da ta fi kowace jiha matsalar rashin biyan albashin ama'aikata

Daruruwan ma'aikatan gwamnati ne ke fama da rashin samun albashi daga wasu jihohi goma sha biyu na tarayyar Najeriya

Daga cikin jihohin akwai wadanda ma'aikatansu suka share fiye da watanni goma sha biyar ko kwandala basu gani ba da sunan albashi.

Cikin jihohin goma sha biyu, jihar Kogi ce lamarin ya fi kamari duk da kasancewar gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin Muhammad Buhari ta basu gudummawar kudaden tallafi da ake kira Bail Out a turance domin su biya ma'aikatansu.

Wasu daga jihar Kogi inda lamarin ya fi ta'azara sun fadi albarkacin bakinsu. Wani Abdullahi Dan Kano yace wasu sun koma ga Allah domin babu albashi. Wasu ma da suka zo tantancewa sun mutu. Ya roki gwamnan jihar ya yi cikin gaggawa a biya mutane.

Wasu ma cewa suka yi basa cin abinci da kyau saboda rashin kudi. An koro masu 'ya'ya daga makarantu suna zaune gidajensu babu abun yi.

Sai dai gwamnatin jihar tace aikin tantance ma'aikatan bogi ne ya kawo jinkirin biyansu. Onarebul Sha'aban Oyinoyi Sha'aibu mataimaki na musamman ga gwamnan jihar yace an mikawa gwamnan rahoton binciken ma'aikatan bogin. Ta dalilin hakan ana dap da kawo karshen tantancewar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsar da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG