Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirage Marasa Matuka Sun Fara Neman Daliban Chibok


Predator B drone
Predator B drone

​Kwana bayan girke jami’an sojin Amurka a Chadi, tuni sun fara aika jirage marasa matuka a ciki domin neman daliban nan mata sama da 250 da ‘yan Boko Haram suka sace.

Jirgin mara matuki a ciki, kuma wanda baya dauke da makami ya bi sawun wani jirgi mai matuka a ciki, kuma mai injina biyu, yanzu haka suna shawagi a samaniyar Najeriya domin taimakawa Amurka nemo daliban.

Wani kakakin ma’aikatar Tsaron Amurka a Pentagon, yace dakarun Amurka na aika jirage sama da guda a lokaci daya, suna neman yaran, wadanda ‘yan Boko Haram suka sace a watan da ya wuce.

“A halin yanzu, wannan aiki na samaniya ne. Muna amfani ne da jirage masu matuka a ciki, da marasa matuka a ciki, bisa yadda abun ya kama,” yace.

Amma ya kara da cewa neman daliban yana da wahala. “Wajen yana da girma. Yana da wahalar dubawa. Akwai cinkoson bishiyu, saboda haka aikin neman yaran da wahala,” a cewar kakakin.

Daga yanzu, binciken Amurka zai mayar da hankali ne a cikin Najeriya, musamman arewa maso gabashin kasar inda jami’ai suke kyautata zaton daliban suke, kuma an rarraba su.

Duk da cewa babu jirgin dake dauke da makami, dukkaninsu suna dauke da na’u’rorin zamani iri-iri da jami’ai ke fata zasu taimaka wajen gano inda daliban suke.

Ya zuwa yanzu, jami’ai basu gano komai ba.
XS
SM
MD
LG