Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Rasha Sun Tashi daga Iran Sun Kai Hari Aleppo Kasar Siriya


Jiragen yakin Rasha
Jiragen yakin Rasha

A yau Talata Rasha tace jiragen yakinta sun tashi daga wani sansanin jirage a Iran suka kai farmaki akan mayakan kungiyar ISIS a Syria.

Rundunar ta Rasha ta dade tana irin wa’yannan hare hare da nufin taimakawa gwamnatin Syria ta shugaba Bashar Al-Assad tun Satumban bara. Wannan Talata ce karo na farko da jiragen Rasaha suka fadada haren haren nasu zuwa wata kasar waje, inda mayakan Rashan suka yi amfani da abokiyar Syriar, Iran suna aikawa da bama-bamai a zango mai nesa.

Jirgin yakin Rasha
Jirgin yakin Rasha


Ma’aikatar tsaron Rasha tace tana wa’yannan hare-haren ne da zummar murkushe kungiyar ISIS da kuma mayakan da wasu kungiyoyin ta’adda dake birnin Aleppo kamar al_Nusrah da sauransu


Wata kafar yada labarai ta gwamnatin Iran , ta ruwaito jawabin shugaban majalisar tsaron kasar, Ali Shamkhani yana cewa Iran da Rasha suna aiki tare don yaki da ta’addanci a Syria kuma suna baiwa juna daman amfani da kasashensu wurin aiwatar da ayyukansu.

XS
SM
MD
LG