Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Rasha Ya Fadi Da Mutane 224 A Misira


Jirgin Rasha wanda ya fadi a Misira.
Jirgin Rasha wanda ya fadi a Misira.

Kasar Rasha ta ga wani mummunan bala'i bayan da jirgin wani kamfanin kasar ya rikito da mutane 224 kuma ana jin babu wanda ya rayu.

Firaministan Masar Sharif Ismail ya tabbatar da faduwar wani jirgin Rasha na matafiya samfurin jet mai dauke da mutane 224, kasa da rabin sa'a guda bayan da jirgin ya tashi daga birnin shakatawar nan na Sham El-Sheikh kan hanyarsa ta zuwa gida a yau dinnan Asabar.

Rahotanni na nuna cewa dukkannin mutanen cikin jirgin sun hallaka.

Jirgin na Airbus mai lambar tafiya A-321, ya kama hanyar zuwa St. Petersburg ne, dauke da yara 17 da 'yan yawon bude ido 217, da kuma ma'aikatan jirgin 7. 'Yan ayyukan agaji na Masar da tuni su ka isa wurin, sun ce har sun fara zakulo gawarwaki daga tarkacen jirgin.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ayyana yau Lahadi a zaman ranar makokin wadanda su ka mutu a hadarin jirgin.

Hukumomin Masar sun ce jirgin a rikito ne a wani wuri mai cike da tsaunuka, wanda ake kiransa Hassana, mai tazarar kilomita 35 kudu da Al Arish, birni mafi girma a yankin Sinai, wanda ke daura da gabar Tekun Mediterrenian.

Wani karamin kamfanin jirgin saman Rasha ne mai suna Kogalymavia, wanda kuma ake kiransa Kolavia, ne ke da jirgin.

Ba a san dalilin faduwar jirgin ba, kodayake hukumomi sun ce ba harbo jirgin aka yi ba. Ya kasa tuntubar sashin kula da tashi da saukar jirgi ya kuma bace daga mahangar rada bayan da ya kai mita 9,100 a sama.

Wasu rahotanni na nuna cewa matukin jirgin ya koka kan wata matsala ta hanyar sakon waya sannan ya bukaci sanin wurin sauka mafi kusa.

XS
SM
MD
LG