Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Yakin Amurka Ya Nufi Yankin Pacific


Jirgin yakin Amurka
Jirgin yakin Amurka

Jiya Litinin Amurka ta tabbatarwa da kawayenta cewar rukunin rundunar mayankan ruwa na USS Carl Vinson ya nufi arewacin yankin Pacific don hana Koriya ta Arewa ci gaba shirinta na makaman nukiliya.

Amma wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan kwanaki da bayanai ke nunin cewa jirgin mai daukar jiragen yaki da wasu jiragen ruwa sun kama hanyarsu zuwa yankin.

Ranar 11 ga wannan watan da muke ciki ne shugaba Donald Trump ya ce zamu aika da Armada, wato babban jirgin yakin Amurka, kwanaki uku kenan bayan da jirgin ya bar kasar Singapore.

Kwamandan sojin Amurka a yankin Pacific, Admiral Harry Harris, ya fada aranar tara ga watan Afrilu cewar ya umarci rukunin mayakan ruwan da su nufi arewa bayan sun bar Singapore kuma wannan na nuna ba za a ci gaba da tsarin farko na zuwa gabar Australia ba.

A jiya Laraba dai, jami’an Amurka sun yi ta kokarin fayyace labarai masu cin karo da juna a kan inda rukunin mayakan ruwan suke.

Kakakin fadar White House Sean Spicer, ya tabbatar da maganar shugaba Trump cewar sun tura jiragen yaki. Yace wannan itace gaskiyar Magana kuma hakan ne ke faruwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG