Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Litinin aka fara jigilar 'yan gudun hijira daga Girka zuwa Turkiya


'Yan gudun hijira dake kushewa kwashesu daga Girka zuwa Turkiya. Kusan daukansu 'yan asalin kasr Pakistan ne
'Yan gudun hijira dake kushewa kwashesu daga Girka zuwa Turkiya. Kusan daukansu 'yan asalin kasr Pakistan ne

A jiya Litinin kasar Girka da Kungiyar Tarayyar Turai sun fara jigilar kwashe ‘yan gudun hijira daga tsibiran Lesbos da Chios zuwa Turkiyya, bisa yarjejeniyar nan mai cike da rudani da aka cimma a watan Maris da ya gabata, a tsakanin gwamantin Turkiya da Tarayyar Turai.

Duk da hasashen yiwuwar rikici, jigilar bakin a jiya ta yiwu lami-lafiya a Lesbos din, in ka dauke wasu tsirarun masu zanga-zangar nuna adawa da yarjejeniyar da suka taru a gabar tekun. An dai fara dibar bakin ne a cikin motar safa a yammacin shekaran jiya daga sansanin dake Moria, zuwa gabar tekun Mytlini inda jiragen ke jiransu.

Wani jami’in Girka ya fadawa Muryar Amurka cewa, mutane 202 ne suka fara yin gaba a cikin jiragen ruwa guda 3. Sai kuma wasu jirage biyu dauke da mutane 136 suka bi bayansu. Jirgi daya kuma mai dauke da mutane 66 ya tashi ne daga tekun Chios a jiya Litinin.

Jami’in ya bayyana cewa, wadanda aka fara yin gaba da su din sun shigar da koken neman mafaka ne, sannan kusan gaba dayansu ‘yan asalin kasar Pakistan ne, in ka dauke wasu ‘yan Syria guda 2 da suka zabi Turkiyya bisa dalilan da su ke da nasaba iyalansu.

XS
SM
MD
LG