Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JNI Ta Bayar Da Shawara Kan Tsaro


Muhammadu Saad Abubakar III
Muhammadu Saad Abubakar III

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ta ba da shawarar cewa a canza salon ayyukan tabbatar da tsaro a Nijeriya.

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana takaicinta kan yadda aka kasa samun ingantaccen yanayin tsaro a Nijeriya duk kuwa da dinbin kudaden da ake kashewa kan albashi da kuma kayan aikin jami’an tsaro na musamman da sauran al’amuran da su ka jibanci tabbatar da tsaron. Kungiyar ta ce hasali ma da bukatar gwamnatin Nijeriya ta canza salo idan ba haka ba kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.

Da ya ke bayani ma wakilinmu da ke Kaduna Lawal Isah Ikarah, babban Sakataren kungiyar Dr. Khalil Aliyu Abubakar ya yi takaicin yadda ya ce bayan kashe dinbin kudi ba tare da an ga sakamakon kirki ba, ana kuma gallaza ba wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Ya ce an kewaye yankin na arewa maso gabashin Nijeriya da jami’an tsaro amma duk da haka sai ka ji ana ta kai hare-hare. Ya ce to ko aljani ne ke kai harin? Don haka ya yi kira ga hukumomi da su yi la’akari da cewa tsarinsu da mishkila.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dr. Khaleel ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su rinka mutunta al’adun mutane da addinansu a yayin gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro. Ya ce kamata ya yi jami’an tsaro su rinka tuna cewa bin abu cikin lalama da siyasa ya fi duk wani amfani da karfi da barazana da kuma tursasawa.
XS
SM
MD
LG