Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Ya Gargadi Turai Akan Kasar Rasha


Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden
Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden

Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi kasashen Turai yau Laraba da su kula kar kasar Rasha ta yi masu katsalandan a harkokin zabensu, kamar yadda a cewar hukumomin leken asirin Amurka su ka yi imanin cewa Rasha ta yi a zaben Shugaban kasar Amurka na watan Nuwamba, wanda ya yi sanadin nasarar Donald Trump.

"Yayin da kasashe da dama a Turai ke shirin gudanar da zabe a wannan shekarar, ya kamata mu yi shirin sake fuskantar yinkurin Rasha na yin katsalandan cikin harkokin demokaradiyya. Hakan zai sake faruwa, ina tabbatar ma ku," a cewar Biden a jawabinsa na karshe a Davos, Switzerland.

Ya cigaba da zargin Rasha da kokarin ruguza abin da ya kira "manufofin masu ra'ayin sassauci a duniya" don a koma yanayin baya, lokacin da kasashe masu karfi ke juya sauran kasashen duniya yadda su ka ga dama. Baya ga auna jam'iyyar Democrat da ya ce ta yi, Biden ya kuma yi nuni da takalar makwabtanta da Rasha ke yi, ciki har da take-takenta a Ukraine, da kuma amfani da albarkatun makamashi a matsayin abin tankwasa wasu kasashe.

Rasha dai ta yi watsi da zargin hukumar leken asirin tsaron kasa ta Amurka na cewa ta yi katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka da zummar taimakon Trump.

Biden ya kuma bayar da tabbaci ga kasashen da ke cikin kungiyar kawancen NATO cewa Amurka za ta cigaba da bayar da himma wajen raya kungiyar. Yayin yakin neman zabe, Trump ya ce yayin NATO ya wuce sannan ya ce AMurka ba za ta rinka kare duk wata kasar NATO da ba ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba.

XS
SM
MD
LG