Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kerry Ya Bayyana Matakan da Zasu Kawo Karshen Rikicin Yahudawa da Falasdinawa


'Yansandan kwantar da tarzoma na Israila
'Yansandan kwantar da tarzoma na Israila

Sakataren harkokin wajem Amurka John Kerry ya bayyana matakan da yakamata a dauka saboda kawo karshen rikicin dake tsakanin Yahudawa da Falasdinawa

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana matakan da ya kamata a dauka bisa taka-tsan-tsan don kashe wutar rikicin Yahudawa da Falasdinawa.

Ya bayyana haka ne a ganawar sa’o’i 4 da yayi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu jiya alhamis a birnin Berlin.

Mista Kerry ya tsara yadda ya kamata ya tari shugaban FalasdinawaMahmoud Abbas da Sarkin Abdullah na Jordan a taron tattaunawar su a ranar Asabar a Amman babban birnin kasar.

Sakataren wajen Amurkan ya kara da cewa, lokaci yayi da Falasdinawa da Yahudawan za su rungumi juna ba kushe da yin tambayoyin da basu da tushe balle a sami amsa a kai.

Sannan su tsayar da rikicin da a kalla ya ci rayukan mutanen Isra’ila guda 50 da na Falasdinawa 50

Netanyahu ya lafta alhakin wannan rikici akan yadda Falasdinawa ke shirya labarai da jita-jitar karerayin da ke sa matasansu daukar makami.

Ya kuma bada bayanin yadda wani ‘dan ta’adda ya so ya tada motar Bas din yara ‘yan makaranta

XS
SM
MD
LG