Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kada Wani Ya Bayyana Sakamakon Zabe – Jega


Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega a wajen taron manema labarai
Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega a wajen taron manema labarai

Yau aka shiga rana ta biyu da ci gaba da kada kuri'u a wasu sassan Najeriya bayan da hukumar zabe ta kara wa'adin rufe rumfunan zabe zuwa yau lahadi.

Shugaban Hukumar zaben Najerya INEC, Attahiru Jega, ya ce kada wani ya kuskura ya bayyana sakamakon zabe har sai hukumar ta fitar da sakamakon a hukumance.

Farfesa Jega ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar domin bayyana yadda zabe ke tafiya na kasar.

“Hukumar zabe ta INEC ce kawai doka ta baiwa damar bayyana sakamon zabe, laifi ne wani ya yi riga-malam-masallaci.” In ji Jega.

Game da tambayar da aka masa kan rashin aikin wasu na’urorin tantance masu kati, Jega ya hukumar na kan biciken yadda hakan ta faru.

“Ana kan binciken dalilin da ya sa na’urorin tantane katin zabe ta suka samu tangarda.”

Shugaban hukumar har ila yau ya yi karin bayani kan dalilin da ya sa aka kara lokacin kammala zaben zuwa ranar lahadi.

“Saboda matsalolin da aka fuskanta, ba a samu damar kammala zabe a jiya ba a wasu mazabu ‘yan kadan, kuma ana gudanar da zabe yanzu haka.” Jega ya ce.

Yanzu haka dai ana can ana kidayar kuri’a a ofisoshin jihohin hukumin a cewar Jega.

“Rahotannin da mu ke samu daga ofisoshinmu a duk fadin kasa na cewa an fara tattara kuri’u kuma koma yana tafiya daidai.” - Jega

XS
SM
MD
LG