Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dokokin Neja Ya Bayyana Dalilin Karbar Matsayin Mukaddashin Gwamna


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Barrister Adamu Usman kakakin majalisar dokokin jihar Neja yace a iya saninsa mataimakin gwamnan ya nemi izinin yin tafiya daga wurin gwamnan jihar.

Kakakin yayi jawabi ne a zauren majalisar jihar inda ya bayyana dalilin da ya sa ya zama mukaddashin gwamna yayin da gwamnan jihar yake yin aikin ummra a kasar Saudiya.

Jawabin ya samo asali ne sabili da ziyarar da shugabannin PDP suka kai masa na nuna goyon bayansu da korar wasu 'yan majalisa biyu da suka canza sheka zuwa jam'iyyar adawa. Yace shi bai damu da surutai ba domin sha'ani ne na mulki.

Dangane da yin watsi da mataimakin gwamnan jihar, sai yace shi mataimakin ya rubutawa gwamnan zai yi tafiya dalili ke nan da aka bashi jihar ya rike. Idan gwamna da mataimkinsa basa nan ai ba za'a bar jihar ba shugabanci ba.

Shi ma shugaban kwamitin labarai na majalisar Bello Agwara ya nace cewa abun da gwamnan yayi yana kan doka domin mataimakin gwamnan ya riga ya rubuta cewa zai yi tafiya..

To saidai ra'ayin 'yan majalisar bai zo daya ba akan batun. Isa Kawu na majalisar yace akwai mataimakin gwamna a gari saboda haka bai kamata a ba kakakin majalisar mukaddashin gwamna ba. Idan kakakin nada hujja cewa lokacin da gwamnan zai yi tafiya mataimakinsa baya nan to sai ya rike amma idan yana nan bai kamata ba.

A karshen makon jiya ne mataimakin gwamnan Alhaji Ahmed Musa Ibeto ya shaidawa manema labarai cewa ya nemi izinin yin tafiya daga wajen gwamnan har sau biyu amma bai bashi izini ba. Yace bai yi tafiya din ba amma kuma sai gashi gwamnan ya mikawa kakakin majalisar mulkin jihar. Yace zasu zauna a jam'iyyarsa su duba lamarin.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

XS
SM
MD
LG