Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: Shugaba Paul Biya Ya Tallafawa Wadanda ‘Yan Boko Haram Suka Kama


Shugaban Kamaru, Paul Biya
Shugaban Kamaru, Paul Biya

Shugaban kasar Kamar Paul Biya ya taimakawa mutanen nan shida da suka shafe sama da kwanaki dari biyu a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram kafin aka ceto su.

Shugaban kasar ya tura wani kwamiti zuwa jihar Arewa mai nisa, karkashin jagorancin gwamnan jihar, domin mikawa mutanen su shida gudummuwar abin masarufi.

An ba mutanen da suka shafe kwanaki dari biyu da goma sha uku a hannun kungiyar Boko haram gudummuwar ne domin su iya samun abin biyan bukata kafin su iya komawa gudar da harkokinsu na yau da kullum. Gwamnati ta ba mutanen tallafin jaka dari biyar kowannensu.

Kungiyar Boko Haram ta kama mutanen ne da misalin karfe goma na safe a kan hanyarsu zuwa garin Kuseri daga Marwa ta shiga da su jeji inda tayi garkuwa dasu na tsawon wadannan kwanaki kafin rundunar tsaron hadin guiwa ta ceto su.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mohammed Awal Garba ya aiki daga Yaounde, Kamaru.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG