Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Ya Kera Agogon Hannu Mai Kwakwalwa


Kamfanin Apple
Kamfanin Apple

Katafaren kamfanin nan mai kirkiro naurori masu kwakwalwa da aka sani da suna Apple na Amurka ya kirkiro agogon hannu mai kwakwalwa da za'a fara sayarwa shekara mai zuwa.

Katafaren kamfanin kere-kere na Amurka Apple ya bude wani sabon babi a harkokin kasuwancinsa, mataki na farko da ya dauka cikin shekarun nan a bikin baje agogon hanu mai kwakwalwa.

Wannan agogo shine na’ura ta farko da kamfanin zai kera karkashin jagorancin Tim Cook, wanda ya karbi jagorancin kamfanin a shekara ta 2011 makonni kamin mutuwar Steve Job daya daga cikin wadanda suka kafa kamfanin.

Agogon wanda ana iya daurashi zai hada ayyukan sa ido gameda koshin lafiya da kuma tsarawa da budewa mutum kofar daki a O’tel. Ana sa ran kamfanin zai fara sayar da gogon cikin shekara mai zuwa kan kudi dalar Amurka 349.

Jiya Talata shugaban kamfanin Tim Cook ya gabatar da agogon a wani taron da ake yi duk shekara na sabbin kere-kere a Cupertino dake cikin jihar California. Hakan ya biyo bayan gabatar da bayanai kan kwaskwarima da aka yiwa wayar cellular Iphone mai farin jinni.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG