Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Pfizer Ya Fara Biyan Diyya A Kano


Kamfanin Pfizer Ya Fara Biyan Diyya A Kano
Kamfanin Pfizer Ya Fara Biyan Diyya A Kano

Kamfanin ya bayarda dalar Amurka dubu 175, kimanin Naira Miliyan 27, ga iyalan wasu yara hudu da suka mutu a lokacin gwajin maganin Trovan

Kamfanin sarrafa magunguna na Pfizer na nan Amurka yace ya fara biyan diyya ga mutanen da abin ya shafa lokacin gwajin wani maganin da ya kashe ya kuma nakkasa wasu a shekarar 1996 a birnin Kano dake arewacin Najeriya.

A yau alhamis, kamfanin Pfizer ya ce ya biya dala dubu 175, kimanin Naira miliyan 27, ga iyalan wasu yara hudu da suka mutu a lokacin gwajin maganin. An biya iyalan yaran a bayan da suka yarda aka gwada jigidar halittarsu ta DNA aka tabbatar da cewa sune ‘yan’uwan yaran.

Wannan kudin wani bangare ne na dala miliyan 75 da Pfizer ya cimma daidaituwa da gwamnatin najeriya a kan zai biya diyya dangane da gwajin maganin.

A shekarar 1996, kamfanin Pfizer yayi gwajin wani maganin kashe kwayar cuta mai suna Trovan da ake ta gardama kansa lokacin barkewar annobar cutar kwalara a Kano. Yara 11 sun mutu bayan da suka sha maganin, wanda aka yi zargin cewa yana janyo nakasa kamar makanta, kurmanci, lalacewar kwakwalwa da shanyewar jiki da wasu illolin da dama.

XS
SM
MD
LG