Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Sayarda Jarirai a Najeriya Sai Kara Bunkasa Sukeyi


Mahukunta na cigaba da samo gidajen da ake ajje mata musamman saboda jariran su.
Mahukunta na cigaba da samo gidajen da ake ajje mata musamman saboda jariran su.

Duk da hukumta masu mummunar dabi'ar saida jarirai da akeyi a Najeriya, abun sai kara bunkasa yakeyi.

An fara samun wannan kamfani na saida jarirai ne a jihar Abia a wani lokaci can baya da aka kama wasu mutane kuma aka hukumtasu.

Daga bisani kuma sai aka samu wasu wuraren a jihohin Imo da Enugu, a farkon wannan shekarar kuma sai gashi an sami kamfanin a jihar Ondo.

Yanzu haka kamfani ya bullo a jihar Ogun, shi dai kamfanin na jarirai, wasu mutane ne masamman mata ke tattara mata masu ciki a waje daya, suna kula dasu, sannan da zaran sun haihu sai su karbe jaririn su saida ga mabukata.

A binciken da muka gudanar ya nuna cewa wasu jariran ana sayansu ne domin yin sidabaru, wasu kuma wadanda basu taba haihuwa bane ke sayensu su maida su a matsayin 'yan yansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG