Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Man Fetur a Najeriya Ya Kara Ta'azara


Ministar Man Fetur na Najeriya Diezani Alison-Madueke
Ministar Man Fetur na Najeriya Diezani Alison-Madueke

Kawo yanzu babu wanda zai iya bada wani takamaiman dalilin da ya sa ake cigaba da samun karancin man fetur a Najeriya

Da gwamnati da hukumomin dake kula da harkokin man fetur a kasar babu wanda ya bayar da wani dalilin da ya sa kasar ta shiga cikin mawuyacin karancin man.

Karancin man fetur sai kara muni ya keyi inda lita daya ta cilla zuwa nera dari da arba'in kuma har zuwa dari biyu a bakar kasuwa, wato kasuwar bayan fagge. A hukumance lita daya nera 97 ce. A birnin Abuja layin motoci dake jiran shan mai kan kai wajen kilomita biyu lamarin da ya sa wasu da basa son shiga layi sai su karkata zuwa kasuwar bayan fagge.

Bishir Mashi wani mazaunin Abuja wanda karancin man yana son ya kutunta masa rayuwa. Yace matsalar mai muddin aka shigeta idan ba'a yi gyara ba to an shigeta kenan. Bata da lokacin karewa. Yace kusan sati biyu ke nan ana fama da abu daya. Layin ma na motocin shan man sai karuwa ya keyi. Masu kudi ne ke samun man yanzu. Idan kai baka da kudin kuma dole ka je aikikto yaya zaka yi ke nan? Wasu yanzu da kafa suke takawa daga gidajensu zuwa ma'aikatarsu su kuma taka komawa gidajensu. Dole sai an yi gyara a ma'aikatar mai.

Usman Sha'aibu Ladan su dake sayarwa a bayan fagge sunce da tsada suka sayo man kuma dole su sayarda tsada. Dangane da dalilin da ke kawo matsalar man sai Ladan yace rashawa da cin hanci ke kawowa. Babu wani abu kuma. Yace duk matsalolin kasar ma basa wuce cin hanci da karbar rashawa.

Shugaban kungiyar dilallalen man fetur Aminu Abdulkadir ya danganta matsalar da fasa bututun mai da dakatar da sakataren kula da farashin man. Yace idan ka dauki hanyar Kaduna zuwa Jos NNPC ta yi kokari ta gyara bututun da aka fasa. Amma idan mutun ya je Fatakwal duk bututun da suka taso daga nan suka ratsa Aba, Makurdi har Yola babu wadanda ke aiki bayan har Aba. Duk sauran babu. Sabili da haka tankunan da aka yi domin su dauki mai daga dipo zuwa gidajen mai wato kusan daukan kashi talatin kenan sai gashi yau an wayi gari suna yin aikin dari bisa dari. Tun da tankuna suka koma yin aikin bututun mai dole a samu matsala.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG