Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasa Aiwatarda Yarjejeniyar Kwango-Kinshasa Cikas ne Ga Ci Gaban Kasar


Bisa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnati da gamayyar ‘yan adawa, kamata yayi bangarorin biyu su kafa gwamnatin rikon kwarya a karkashin sabon firayin minista har sai an yi zabe zuwa karshen shekarar nan.

Amurka ta nuna damuwarta akan yadda bangaren gwamnatin Kwango-Kinshasa da na gamayyar jam’iyyun ‘yan adawa suka kasa aiwatar da yarjejeniyar sauya ragamar mulkin kasar da suka rattabawa hannu a watan Disambar bara bayan watanin da aka kwashe ana dauki ba dadi a kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dora laifin akan bangarorin biyu saboda gazawar da suka yi wajen cimma matsaya akan yarjejeniyar, wacce ta hada da nadin sabon firai minista.

“Kasa aiwatar da yarjejeniyar na nuna dakilewa ‘yan kasar Kwango muradunsu kuma ya kawo tsaiko ga cigaban da aka samu a kasar ya zuwa yanzu" a cewar kakakin ma’aikatar harakokin wajen Amurka, Mark Toner.

Ya kamata shugaba Joseph Kabila ya sauka daga kan karagar mulki tun ranar 19 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, wato karshen wa’adinsa na biyu, amma kuma aka dage zaben shugaban kasan da ya kamata ya maye gurbinsa kuma har yanzu Kabila na nan a matsayin shugaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG