Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Angola ta sami ci gaba a yaki da cutar Polio


Wadansu kananan yara a wajen rigakafin shan inna
Wadansu kananan yara a wajen rigakafin shan inna
Kasar Angola ta cika shekara daya ba tare da an sami ko karamin yaro daya dauke da kwayar cutar shan inna ba. Bisa wannan dalili ana ganin kasar tana dab da shiga jerin kasashen da suka shawo kan yaduwar wannan cutar.

Wata sanarwar da ta fito daga ma’aikatar lafiya ta kasar Angola da hukumar lafiya ta duniya da kuma asusun tallafawa kananan yara UNICEF suka bayar na nuni da cewa, an sami raguwar kananan yaran dake dauke da wannan cutar daga 33 a shekara ta dubu biyu da goma zuwa biyar a shekara ta dubu biyu da goma sha daya, yayinda ba a sami yaro ko guda daya dauke da kwayar cutar ba a shekarar nan ta dubu biyu da goma sha biyu.

Sakamakon binckin dakunan kwakwa ya nuna cewa, an sami yaro na karshe dake dauke da kwayar cutar a watan Yuli shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Bincike na nuni da cewa, kasar Angola ta sami nasarar shawo kan cutar ne sabili da irin gangamin da tayi da kyakkyawan sa ido a aikin rigakafi, yayinda kuma aka inganta kula da lafiyar al’umma ta wajen samar da ruwa mai tsabta da kuma tsabtace muhalli.

Kasar Angola ta kuma dauki kwararan matakan shawo kan yada cutar a yankunan da aka sami yaran dake dauke da ita, ta wajen maida hankali wajen yin rigakafi a kauyukan dake kan iyaka. Kasar ta kashe kudi kan rigakafi tare da yin amfani da dubban ma’aikatan lafiya da masu aikin sa kai, inda aka bi tituna da kasuwanni da gidaje ana yiwa kananan yara kasa da shekaru biyar rigakafi.

Rahoton shirin shawo kan cutar shan inna na duniya na shekara ta dubu biyu da goma sha biyu na nuni da cewa, an sami kananan yara 103 dauke da kwayar cutar I zuwa ranar 1 ga watan Agusta 2012, yayinda matsalar tafi muni a kasashe uku da suka hada da Najeriya da Pakistan da kuma Afghanistan.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG