Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Birtaniya Zata Fara Tantance Wadanda Suka Shiga Kasarta daga Kasashen Yammacin Afirka Masu Fama da Cutar Ebola


Wani cikin sojojin da suka isa Liberiya domin yakar cutar ebola
Wani cikin sojojin da suka isa Liberiya domin yakar cutar ebola

A kokarin dakile yaduwar cutar ebola a kasar Birtaniya mahukuntar kasar zasu fara tantance duk wadanda suka shiga kasar daga kasashen yammacin Afirka dake fama da cutar

Kasar Birtaniya zata fara tantance fasinjojin da suka shiga kasar daga kasashen yammacin Afirka a filayen saukar jiragen sama biyu.

Wakazalika zata tantance masu shigowa daga tashar jirgin kasa da ta hada kasar da yammacin turai.

A wata sabuwa kuma wani dan Birtaniya da ake zaton yana da cutar ebola ya mutu a Macedonia.

Jami’an asibitin Macedonia sun ce mutumin ya nuna alamun kamuwa da cutar ebola wadanda suka hada da zazzabi, amai da fitar da jinni. Wadanda suka kaishi asibiti an waresu wuri guda kana otel din da ya sauka a Skopje an killayeshi.

Ba’a sani ba ko mutumin ya ziyarci nahiyar Afirka kafin ya shiga jirgi zuwa Macedonia.

Amurka ma zata fara tantance wadanda suka fito daga kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo a tashar jirage ta JFK dake New York daga wannan Asabar. Za’a kuma soma tantance mutane a wasu tashoshi guda hudu mako mai zuwa.

Wata mai aikin jinya a Madrid kasar Spain tana cikin wani mawuyacin rashin lafiya bayan da tayi jinyar wasu fada fada da suka kamu da cutar ebola.

Kawo yanzu ebola ta hallaka akalla mutane 3,900 a yammacin Afirka kuma ta bulla a wasu kasashe da dama har da Amurka da Spain.

XS
SM
MD
LG