Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Habasha tana shirin rantsar da sabon Firai Minista


Akwati dauke da gawar Meles Zenawi
Akwati dauke da gawar Meles Zenawi
Majalisar dokokin kasar Habasha ko Ethiopia na can tana shirin soma wani zaman gaggawa domin rantsar da mutumen da zai maye gurbin firai ministan kasar da ya rasu shekaran jiya Litinin, Meles Zenawi.

Ana sa ran wanda za’a rantsar din shine Hailemariam Desalegn (Desalin) wanda tun 2010 yake zaman mataimakin firai ministan, kuma shine yanzu zai cike sauran wa’adin mulki na shi marigayin, wa’adin da zai kare a 2015.

A jiya Talata ne dai aka dawo da gawar Mr. Meles, wanda ya share fiye da shekaru ashirin yana mulkin Ethiopia, a nan babban birnin kasar na Addis Ababa, inda dubban mutane suka tarbi gawar, da yawansu suna ta shara kuka, wasu na dauke da manyan hotunansa, wasu na dauke da kyadir mai ci da wuta.

Shugabannin kasashen duniya da dama sun yi ta bayyana jinjina ga marigayin saboda yadda ya habaka tattalin arzikin kasar tashi, da kuma rawar da ya taka wajen inganta harkokin tsaro a wannan bangaren na nahiyar Afrika.

A daren Litinin din shekaranjiya ne Mr. Meles, 57, ya rasu yayinda yake a wani assibitin kasashen Turai.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG