Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Switzerland Zata Mayarwa Najeriya Dala Miliyan 321


ma'aikatan banki na kirga kudi.
ma'aikatan banki na kirga kudi.

Kwanan nan gwamnatin kasar Switzerland za ta maida wa Nigeria wasu makudan kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka Miliyan 321 bisa wata yarjejeniyar da suka kulla kamar yadda kakakin shugaban Najeriya Garba Shehu ya bayyana.

Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a ranar Talatar shekaran jiya tsakanin babban lauyan gwamantin Najeriya (Atoni-Janar) Abubakar Malami, da kuma Ministan harkokin wajen Switzerland Didier Burkhalter.

Kudaden dai wadanda suka rage ne daga cikin wadanda tsohon shugaban kasar a karkashin mulkin soji Janar Sani Abacha ya boye ne a bankunan kasar. Garba Shehu yace suna sa ran dawowar kudin zuwa gida nan ba da dadewa ba.

Sai dai mafi yawancin ‘yan Najeriya na fargabar da wuya ayi amfani da kudin ta hanyar da talaka zai mora, domin kuwa suna nuna cewa ko kason farko na irin wadannan kudade da aka taba cetowa Najeriya, ba talakan da ya mora domin kuma sun sake batan dabo ne.

XS
SM
MD
LG