Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Da Ke Taimakawa Somalia Da Tsaro Za Su Janye


Amurka da Kungiyar Tarayyar Afrika sun amince cewar lokacin da yakamata Somalia ta dauki dawainiyar tsaron kanta na ci gaba da karatowa.

A wani taron tattaunawa ta wayar tarho da dakarun hadin guiwan Amurka da Afrika ta AFRICOM ta shirya a Stuttgart a Jamus, komandan dakarun AFRICOM Thomas Waldhauser yace sanarwa da Amurka ta yi a cikin wannan lokaci na aikewa da dakaru 40 zuwa Somalia bai canza salon da ake dauka ba.

Amurka zata ci gaba da taimakawa ma’aikatar sojin Somalia da basu horarwa don ta iya samun kayan yaki da zata taimakawa rundunarta. Yace wannan na cikin taimako da ba a saba yi ba, wanda yake tasiri na tsawon lokaci inji Waldhauser.


Somalia da kawayenta na kasa da kasa suna aiki tare don horar da sojojin kasar dubu 28 bayan shekaru da dama da yakin basasa da kuma rikici da kasar take fama dasu. Kungiyar yan ta’addan al-Shabab tana ci gaba da rike a kalla kashi goma cikin dari na kasar tana kuma kai hare hare masu auna sojoji da fararen hula.

Somalia dai ta dogara ne kacokan a kan rundunar kiyayaye zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afrika dubu 22 wato AMISOM a takaice da suke aiki a Somalia.

An fara ganin yiwuwar samun zaman lafiya a Somalia ne daga zaben shekarar 2017 da aka yi cikin lumana da kuma mika mulki ga sabon shugaban kasa Mohamed Abdullahi Mohamed cikin ruwan sanyi.

Kasar tana ganin gindaya lokacin janye sojojin zaman lafiyar zai taimakawa gwamnatin Somalia ta karfafa hukumominta su tinkari ayyukan ta’addanci dake barazana ga kasar da kuma warware rikicin cikin gida dake kawo rarraban kawuna a cikin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG