Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya 170 Sun Saka Hanu Kan Yarjejeniyar Dakatarda Dumamar Yanayi


Shugaban Faransa Francois Hollande, da wasu shugabannin kasashen duniya., lokacinda aka cimma yarjejeniyar a bara.
Shugaban Faransa Francois Hollande, da wasu shugabannin kasashen duniya., lokacinda aka cimma yarjejeniyar a bara.

Jiya jumma'a ne kasashen suka yi bikin sanya hanun a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York

Fiyeda kasashen duniya 170 ne a jiya jumma'a, suka rattaba hanu kan yarjejeniyar da zata takaita dumamar yanayi da sakewar yanayi a doron kasa.

A karshen bara ne dai aka cimma yarjejeniyar a birnin Paris, amma a jiya ne aka yi bikin sanya hanu akai, a ranar da MDD ta ware a duk shekara, domin maida hankali kan kiyaye muhalli."Lokaci yana neman ya kure mana," babban sakatare na MDD Ban ki-moon yayi gargadi. Ya ci gaba da cewa, "damar rage dumamar yanyi kasa da maki biyu a sikelin Celcius, yana kara kurewa. Zamanin fidda gurbatacciyar iska ba tareda anga wata illa ba ya wuce." Inji Mr. Ban.
Yace tilas ne kasashen duniya su kara zake dantse wajen sauya harkokin tattalin arzikinsu daga dogaro da masana'antu da wasu hanyoyi wadanda suke gurbata yanayi. Daga nan yayi kira da a taimakawa kasashe masu tasowa su canza daga hanyoyi da suke illa ga muhalli.

Wadanda da suke sanya hanu kan yarjejeniyar, sune kamar kashi 93 cikin dari na kasashe da suke fidda gurbatacciyar iskar. Kuma sune kasashe na farko da suka rattaba hanu kan yarjejenyar.
Kasashe da suka fi ko wadanane fitarda gurbatacciyar iskar, sun hada da China da Amurka, wadanda suke fitar da kashi 40 cikin dari na wannan iska.

Duka kasashen biyu, sun yi kiran da a fara aiawatar da yarjejeniyar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG