Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Kungiyar ECOWAS Sun Maida Hankali Kan Harkokin Noma


Wasu Shugabannin ECOWAS
Wasu Shugabannin ECOWAS

Dan majalisar dokokin kungiyar gamayyar kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS mai wakiltar Najeriya yace sun fara sanya kudade masu yawa a harkokin noma idan ba haka ba kasashen zasu cigaba da dogaro ga kasashen waje

Yace hakan na nufin maimakon su ciyar da kansu zasu cigaba da dogaro ga kasashen waje wajen samar ma al'ummominsu abinci.

Majalisar ta ECOWAS ta umurci kasashen su dinga bada kashi goma na kasafin kudinsu na kowace shekara kan harkokin noma. Wannan matakin da kungiyar ta dauka ya biyo bayan aikin wasu kwamitoci biyar da ta kafa wadanda suka yi aikinsu a kasar Senegal. Sun maida hankali ne kan karkata manufar ECOWAS a kan aikin gona.

Dr Huseni Hassan yace za'a iya cimma burin koda ba zasu iya bada kashi goma ba na kasafin kudinsu. Idan suka iya hada kashi biyar zai tallafa a wannan tafiyar da suka sa gaba. Hakan kuma zai shafi miliyoyin jama'a da za'a iya taimakawa. Yace za'a kuma iya korar yunwa.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG