Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Tafkin Chadi Za Su Gana a Taron MDD


Shugabannin kasashen Tafkin Chadi
Shugabannin kasashen Tafkin Chadi

Yayin da ake shirin kaddamar da taron koli na Majalisar DinkiN Duniya (MDD) a birnin New York da ke Amurka, hukumar da ke kula da asusun yawan al’uma a duniya, ta shirya wani taro da zai hada kasashen da ke kusa da tafkin Chadi domin tattaunawa kan matsalolin tsaro.

A na san taron zai ta’allaka ne kan yadda za a shawo kan rikicin ta hanyar yin amfani da muradun karni da aka cimma da kuma bin tafarkin muradun ci gaba masu dorewa da ake so a kai ga nan da 2030.

Masu tsautsauran ra’ayi kan yi amfani da matasa a yankunan kasashen Kamaru da Najeriya da Chadi da Nijar domin karkata su zuwa ayyukan ta’addanci.

Ya zuwa yanzu rikici a wadannan yankuna ya daidaita al’umomi da dama, musamman mata, inda yanzu haka a tsakanin watan Aprilun 2015 zuwa yanzu, an sace mata da ‘yan mata sama da 2,000 kamar yadda kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty ta bayyana.

Wannan zama da kasashen za su yi gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya, zai ba da dama a shata hanyoyin da za a bi wajen karfafa matasa tare da karesu daga fadawa harkokin ayyukan ta’addanci.

Taken taron wanda za a yi a ranar 26 ga watan nan na Satumba a birnin New York, shi ne yadda za a yi amfani da matasa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasashen da ke kusa da tafkin Chadi da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Ana kuma sa ran shugaban Jamhuriyar Benin, Boni Yayi da na Kamaru, Paul Biya da na Chadi Idriss Deby Itno da na Nijar Mahamadou Issoufou da kuma na Najeriya, Muhammadu Buhari, za su gabatar da jawabansu a gaban taron.

Kana shugaban hukumar asusun yawan al’uma na Majalisar Dinkin Duniya, Dr. Babatunde Osotimehin shima zai gabatar da na sa jawabin.

XS
SM
MD
LG