Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Kudi Na Tarayyar Turai Sun Amince Da Gagarumin Shirin Ceto Takardar Kudin Euro


Wannan shiri da zai lashe kudi har dala miliyan dubu 960 an tsara shi da nufin hana matsalar kudi ta kasar Girka yaduwa zuwa sauran kasashe masu amfani da takardar kudi ta Euro.

Ministocin kudi na kasashen Tarayyar Turai sun amince da wani gagarumin shirin tallafawa takardar kudin Euro wanda zai iya lashe kudi har dala miliyan dubu 960, watau Euro miliyan dubu 750.

Ministocin sun gudanar da taron kolin gaggawa ba tsayawa a kokarinsu na ganin sun cimma yarjejeniya kafin a bude manyan kasuwannin hada-hadar kudi na kasashen Asiya a litinin din nan.

Wannan shirin da ya kunshi bayar da rance daga kasa guda zuwa guda, da kuma tsaya ma wata kasa domin ta karbi bashi, an tsara shi da nufin hana rikicin nauyin bashi dake kan kasar Girka yaduwa zuwa sauran kasashe masu yin amfani da takardar kudi ta Euro.

Akasarin wannan kudi zai fito ne daga aljihun Kungiyar Tarayyar Turai, yayin da Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF, shi ma zai tallafa da wani kason.

Jim kadan a bayan da aka samu sanarwar cimma wannan yarjejeniya, alkaluman hannayen jari na Nikkei na Tokyo a kasar Japan sun cira sama da kashi daya da rabi cikin 100, yayin da kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Sydney a kasar Australiya ta yi sama da kusan kashi 2 cikin 100.

Masu saye da sayarda hannayen jarin sun fara jan jikinsu daga takardar kudin Euro a bayan da matsalar kudin kasar Girka ta kunno kai. Darajar takardar kudin Euro ta fadi da kashi 4 cikin 100 a makon da ya shige a bayan da kasuwannin hada-hadar kudade na duniya suka fara nuna damuwar cewa matsalolin Girka zasu iya yaduwa zuwa ga wasu kasashen na Tarayyar Turai wadanda su ma su na da matsalolin kudi, cikinsu har da Spain da Portugal da kuma Ireland.

XS
SM
MD
LG