Accessibility links

Katin Shaida na Zamani na ECOWAS Zai yi Matukar Amfani


Kadre Desire Ouedraogo, shugaban kungiyar ECOWAS.

Kadre Desire Ouedraogo, shugaban kungiyar ECOWAS.

Wannan mataki zai kawar da wulakancin da matafiya ke fuskanta a hannun jami'ai idan sun zo tsallaka kasashe.

A yayin da kungiyar Tarayyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma, ECOWAS, ko CDEAO, ta karbi shawarar bullo da katin shaida irin na zamani domin amfani a tsakanin kasashen yankin, mutane da dama su na tofa albarkacin baki a kan wannan matakin.

Wani direban mota dan kasar Ghana dake jigilar mutane daga Lagos a Najeriya zuwa Accra Ghana, Ali Alhassan, wanda aka fi sani da sunan Ali Fadama, yace ga matafiya irinsu, katin shaidar zai fi amfani da tasiri a saboda zasu fi jimawa a kan takardun Fasfo wadanda su a koyaushe aka zo tsallaka kasa sai an buga musu hatimi, abinda zai sa su cika a cikin kankanin lokaci.

Haka kuma yace matafiya su na fuskantar cin zarafi idan suka zo tsallaka wata kasa da takardun fasfo a saboda sai sun biya kudin cin hanci a yawancin lokuta kafin a buga musu hatimi a kai.

Yace ana matukar wulakanta matafiya a dukkan kasashen yankin Afirka ta Yamma, tare da yin kira ga kungiyar da ta gaggauta aiwatar da wannan mataki nata.

XS
SM
MD
LG