Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba


Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba
Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba

Kwararru sun yi kiran da a yi kokarin kawar da wannan ciwo daga duniya, amma sun ce yin hakan zai yi wuya ba tare da an samu maganin rigakafin kamuwa da shi ba.

Miliyoyin mutane a fadin duniya zasu yi marhabin da kawar da zazzabin maleriya, wanda ke kashe mutane fiye da dubu dari takwas da sittin kowace shekara a fadin duniya, amma masana kiwon lafiya sun ce a yanzu kam ba su ganin za a iya cimma wannan guri.

Wannan ra’ayi na kwararru masu bincike ya sha bambam sosai da muhimmiyar sanarwar da ta fito daga bakin Gidauniyar Bill da Melinda Gates da kuma Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, wadanda suka bayyana aniyarsu ta kawar da wannan ciwo daga bangon duniya.

Editan mujallar kiwon lafiya ta Britniya mai suna Lancet, Richard Horton, ya bayyana wadannan kalamu dake fitowa daga bakin cibiyoyin biyu a zaman “wauta, ba wai jarumtaka ba.” Y ace cimma wannan gurin, musamman ga kasashen bakar fata na Afirka zai zamo mafarki ne kawai, yana mai nuni da rashin cibiyoyin kiwon lafiya masu nagarta a nahiyar, da karancin magunguna da wasunsu.

Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba
Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba

A ranar Jumma’a, mujallar ta Lancet ta nazarci yiwuwar kawar da zazzabin cizon sauron cikin wasu kasidu da ta wallafa. Kwararru sun nazarci batutuwa kamar yiwuwar kawar da ciwon da kuma irin kudin da za a kashe. Kawar da Maleriya zata bukaci kudi fiye da yin maganinta ko shawo kanta, kuma masana tattalin arziki sun yi kashedin cewa ba lallai ne yin hakan zai sa a iya tsimin kudi nan gaba ba.

Koda yake bincike ya nuna cewa zai yiwu a iya kawar da wannan ciwo da sauro ke yadawa a kasashen Latin Amurka da Asiya, wannan abu kusan ba zai yiwu a nahiyar Afirka ba, inda ake samun mafi yawan mutane miliyan 247 masu kamuwa da wannan ciwo kowace shekara a duniya. Ana iya warkar da zazzabin cizon sauro idan aka fara maganinsa da wuri, amma ciwon yana yin mummunar illa ga yara ‘yan kasa da shekara 5 da haihuwa wadanda su suka fi mutuwa a sanadinsa.

Daya daga cikin abubuwan dake kawo cikas shi ne rashin maganin rigakafin kamuwa da maleriya. Har yanzu ana gwajin maganin rigakafin da aka ga alamun zai fi nagarta, kuma shi din ma duk da nagartar tasa, yana aiki a jikin mutane hamsin daga cikin 100 ne kawai wadanda aka yi musu allurer.

Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba
Kawar Da Maleriya Zai Yi Wuya Ba Tare Da Rigakafinsa Ba

Idan an kwatanta za a ga cewa magunguna kala hudu da ake allurer rigakafin cutar shan inna ko Polio da su, sun a aiki a kasha casa’in da biyar daga cikin 100 na wadanda aka bas u magungunan.

Wasu kwararrun kuma sun ce tun da kasashe fiye da 70, cikinsu har da Amurka, Britaniya, Italiya da Singapore, sun riga da sun kawar da zazzabin maleriya daga kasashensu, za a iya cimma tazara sosai ta yin amfani da abubuwan da ake da su a yanzu kamar gidan sauro da magunguna. Bunkasar tattalin arziki da kyautatuwar halin rayuwa ma zasu taimaka.

Haka kuma da yake sauro ne yake yada wannan ciwo, kawar da shi baki daya zai zamo yana da sarkakiya sosai. Ba kamar kwayoyin cutar da mutane ke yadawa da kansu ba, kawar da maleriya na nufin kawar da kwayar cutar dake haddasa wannan ciwo daga jikin dubban miliyoyin sauro.

Richard Tren, darektan wata kungiyar agaji mai zaman kanta da ake kira “Africa Fighting Malaria” yace jami’an kiwon lafiya sun mika wuya ga ‘yan rajin kare muhalli, sun yi watsi da bukatar dake akwai ta bullo da sabbin magungunan kashe kwari. Y ace, “babu ta yadda zaka iya kawar da cutar da wani kwaro ke yadawa ba tare da Karin magungunan kashe kwari ba.”

Yunkurin da aka yi a can baya na kawar da zazzabin cizon sauro a duniya ya ci tura a kasashe masu tasowa. A shekarar 1955, Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta fara gudanar da irin wannan aiki, amma tilas ta watsar da shi a 1969. A 1998, hukumar tare da wasu cibiyoyi sun hada karfi suka bullo da shirin murkushe maleriya mai suna “Roll Back Malaria” amma shekaru a bayan wannan, sai aka gano cewa yawan masu kamuwa da maleriya ya karu fiye da can baya ne ma.



XS
SM
MD
LG