Accessibility links


Shugabannin wasu kasashen afirka zasu yi taro yau alhamis domin tattauna Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda aka kashe mutane fiye da dubu daya a fadan da ake yi tun watan Disamba.
Kungiyar Kasuwar tattalin Arzikin Tsakiyar Afirka, ECCAS, ita ce ta shirya wannan taron da za a yi a Chadi makwabciyar Jamhuriyar.
Ministan yada labarai na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Adrien Poussou, ya fadawa Muryar Amurka cewa shugaba Michel Djotodia, shi ne ya bukaci da a yi wannan taron domin tattauna yadda za a mayarda rundunar sojojin kasashen Afirka zuwa ta aikin kiyaye zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar.
Yace shugaban rikon kwaryar zai kuma bayyanawa shugabannin kasashen yankin irin halin tsaron da ake ciki a Bangui, babban birnin kasar.
Poussou yace babu gaskiya a cikin rahotannin da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayar cewa mahalarta taron zasu tattauna a kan ko ya kamata Mr. Djotodia ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki.
Mr. Djotodia ya karbi ragamar ikon kasar a bayan da ‘yan tawayen kungiyar Seleka wadda Musulmi suka fi yawa a ciki, suka hambarar da shugaba Francois Bozize a watan Maris na bara. Tun daga lokacin, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta tsunduma cikin fitina, akasarinta a tsakanin tsoffin ‘yan tawayen Seleka da kungiyoyin sojojin sa kai na mabiya addinin Kirista.
XS
SM
MD
LG