Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Jinkai Ba Zasu Shiga Aleppo Ba Sai da Izinin Gwamnatin Siriya - MDD


 Staffan de Mistura, manzon MDD na musamman akan Siriya
Staffan de Mistura, manzon MDD na musamman akan Siriya

Jamia’an Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, sun fada yau cewa tawagar ma’aikatan jin kai, a shirye suke su tafi birnin Aleppo dake Arewacin Syria a kowane lokaci domin kai kayan jin kai ga mutanen dake matukar bukatarsu, amma sun kasa yin hakan har sai sun samu izini daga gwamnatin kasar .

Babban jamiin tawagar Jan Egeland ya fada wa manema labarai cewa yana fata a samu damar kai wadannan kayayyaki zuwa gobe Juma’a.

Yace shin wai mutanen da suka ci suka koshi, zasu daina kawo cikas ta hanyar sa siyasa da kawo tarnaki ga ma’aikatan jin kai dake da niyyar taimakawa mata da yara farar hula da yaki ya daidaita a wannan yankin.?

Yace wadannan kayayyakin suna cikin yarjejeniyar da aka kulla na tsagaita bude wuta wadda ta fara aiki ranar Littinin din nan.

Yanzu haka dai an rage kashe-kashe, da kai hari ga makarantu, da kuma asibitoci.

Shugaban tawagar MDD Syria, Staffan de-Mistura, yace wannan yarjejeniyar zata zame wata hanyar canza al’amurra musammam game da wannan yakin na kasar ta Syria wanda aka kwashe shekaru 6 ana gwabzawa. Sai dai shima ya bayyana takaicinsa na rashin ganiN wadannan kayyayyakin jin kai sun isa kan lokaci, yana cewa baiga dalilin da zaisa a sami wannan tsaiko ba.

XS
SM
MD
LG