Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta zargi Saudiya da yin adawa da yarjejeniyar shirin nukiliyarta da kasashen turai


Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif

Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Saudiya da kushewa yarjejeniya da kasarsa ta cimma da kasashen tarayyar yammacin Turai da Rasha

Ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya ce ya zama dole kasar Saudiya ta yi zabi tsakanin marawa ayyukan ta’addanci baya da kuma zamantowa mai samar da zaman lafiya da daidaito a yankin Gabas ta Tsakiya.

A wani bangaren bayyana ra’ayi na jaridar New York Times, Zarif ya soki kasar ta Saudiya kan adawar da ta ke yi da matsayar da aka cimma kan shirin makamashin nukiliyan Iran da sauran kasashen duniya.

Zarif har ila yau ya soki dakarun da Saudiyan ke jagoranta a Yemen da hare-haren da ake kaiwa kan manufofin Iran da kuma turmutsutsun da ya halaka daururuwan mutane a aikin hajjin bara.

A ‘yan shekarun baya nan, ana samun takun-saka tsakanin Iran da Saudiya, wadanda manyan kasashen ne da ke yawan samun rashin jituwa kan rikicin Yemen da Syria.

A makon da ya gabata Saudiyya ta ayyana yanke huldar diplomasiyya da Iran, bayan da aka kaiwa ofishi jakadancinta hari a Tehran, jim kadan bayan da Saudiyyan ta zartar da hukucin kisa kan wani fitaccen malamin Shi’a.

XS
SM
MD
LG