Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin mutane 19,000 aka kashe a Iraqi cikin shekaru biyu - MDD


Mayakan sa kai na kungiyar ISIS da suke kashe mutane a Iraqi
Mayakan sa kai na kungiyar ISIS da suke kashe mutane a Iraqi

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta fada yau Talata cewa kusan mutane 19,000 aka kashe a Iraki tsakanin watan dayan shekarar 2014 zuwa watan okotabr shekarar da ta gabata, yayinda wasu fiye da miliyan 3 su ka rasa matsugunnansu.

Yawaitar tashe-tashen hankulan ya zo kuma daidai da lokacin da ‘yan kungiyar ISIS ke mamaye manyan wurare a arewaci da yammacin Iraki, abinda ya janyo hankalin kasashe a cikin tsakiyar shekarar 2014, lokacin da Amurka kuma ta fara kai wa mayakan hare-hare ta sama a watan Agustan bara waccan.

Duk da cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya yi muni, hakan kwata-kwata bai nuna takamaimai halin kaka-na-kayin da farar hula suka shiga aba a Iraki, a cewar shugaban kungiyar kare hakkokin bil’adama ta MDD Zeid Ra’ad Al-Hussein. Ya ce adadin ya nuna wadanda aka kashe ko suka tagayyara ne kawai sakamakon tashin hankalin, amma akwai wasu da suka mutu sanadiyyra rashin abinci, da ruwan sha, da kuma magunguna.

Rahoton ya kuma ce ana kyautata zaton cewa mayakan suna rike da mutane 3, 500 da suka maida bayi, yawancin su ‘yan kabilar Yazidi ne, kuma suna cigaba da saba da muzanta dokokin kasa-da-kasa na kare hakkokin jama’a. Rahoton ya kuma nuna cewa akwai muzanci da cin mutunci da dakarun dake marawa gwamnati baya ke yi su ma.

XS
SM
MD
LG