Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Yara 20,000 Ke Cikin Fallujah Birnin da Sojojin Iraqi Suka Yiwa Kawanya


Sojojin Iraqi dake yakin kwato Fallujah daga hannun ISIS
Sojojin Iraqi dake yakin kwato Fallujah daga hannun ISIS

Ana kyautata zaton akwai kimanin yara 20,000 da suka makale cikin birnin Fallujah inda dakarun Iraqi suka zafafa kai hari a kokarin da suke yi su kwato birnin daga kungiyar ISIS wadda tayi shekaru biyu tana rike da birnin.

Tun lokacin da dakarun Iraqi suka soma fafatawa a Fallujar mai tazarar kilomita 60 daga Baghdad babban birnin kasar mutane kalilan ne da iyalansu suka samu arcewa daga birnin.

Yawancinsu sun je wasu sansanoni guda biyu wasu kuma sun nemai mafaka da 'yanuwansu kamar yadda asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar. Asusun ya yi kashedin cewa yara suna fuskantar barazanar tilasta masu shiga yakin lamarin da ka iya rabasu da iyalansu.

Kusan mutane 3,700 ne suka samu suka tsere daga birnin Fallujah garin da 'yan darikar Sunni suka fi yawa . Ana tsoron kungiyar ISIS na iya garkuwa da dubban farar hula.

Wadanda suka arce daga birnin sun ce babu isasshen abinci da magani kuma ruwan sha ya gurbace.

Firayim Ministan kasar Haider al Abadi ya gargadi dakarun kasar dake yaki a Fallujah da su yi kokari su kare farar hula.

Wasu yaran da suka samu suka tsere da iyayensu
Wasu yaran da suka samu suka tsere da iyayensu

XS
SM
MD
LG