Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kin biyan haraji da kamfanoni ke yi yana janyo koma bayan tattalin arzikin Afrika


Wani mutum yana canjin dalar Amurka
Wani mutum yana canjin dalar Amurka

Wata kungiyar tada tsimin jama’a dake Amurka tace adadin kudin da ake badda sawunsu ya ninka tallafin kudin da ake ba nahiyar.

Wata kungiyar tada tsimin jama’a dake da zama a nan Amurka tace adadin kudin da ake badda sawunsu zuwa wadansu kasashe tun daga shekara ta dubu da dari tara da saba’in da tara ya ninka tallafin kudin da ake ba nahiyar.

Darektan cibiyar sa ido kan harkokin kudaden kasashen duniya Raymond Baker ya shaidawa Muryar Amurka cewa, cibiyarshi ta hakikanta cewa, an badda sawun akasarin kudin ne domin gudun biyan haraji amma ba cin hanci da rashawa ko kuma rubda ciki da kudin al’umma ba.

Baker yace hanyar da aka fi kaucewa biyan kudin fice ita ce, aki fadin aininin darajar kaya da nufin kin biyan kudin fice da sauran haraji da suka shafi cinikin kasa da kasa.

Bisa ga cewar cibiyar GFI, Najeriya ce kan gaba a wannan fannin inda aka badda sawun kusan dala biliyan casa’in daga shekara ta dubu da dari tara da casa’in zuwa yau.

XS
SM
MD
LG