Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristoci Sun Yi Addu’oi Domin Zaman Lafiya a Najeriya


Birnin Kudus
Birnin Kudus

Kirista da suke ziyara a kasa Mai Tsarki sun yi addu’oi na musamman domin zaman lafiya da hadin kan kasa musamman a arewacin Najeriya inda ake fama da tashe tashen hankali

Kirista da suke ziyara a kasa Mai Tsarki sun yi addu’oi na musamman domin zaman lafiya da hadin kan kasa musamman a arewacin Najeriya inda ake fama da tashe tashen hankali.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa ta wayar tarho, shugaban kungiyar hadin kan Kirista reshen jihar Bauchi Rev Shu’aibu Byel yace sakon da suke tafe dashi shine sakon fatar Alheri da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai dabam dabam musamman Kirista da Musulmi a Najeriya.

Yace Allah a cikin ikonsa ya sanya al’ummar kasar a wuri daya, inda ake kabilu dabam dabam da addinai dabam dabam domin cudanya da juna. Yace nufin Allah ne al’ummar Najeriya su zauna tare lafiya domin ci gaban kasa.

Shugaban kungiyar hadin kan kiristan yace sun bar Najeriya a cikin wani yanayi marar dadi kasancewa a ranar da suka tashi aka kai hare haren boma bomai a jihohin Gombe da Bauchi da ya yi sanadin asarar sama da rayuka talatin.

Mahajjata dari biyu da casa’in da bakwai ne daga jihar Bauchi suka sami tafiya kasa Mai Tsarki bana, kuma suna kyautata zaton tashi zuwa Najeriya ranar biyu ga watan Janairu.

Ga cikakken rahoton da Abdulwahab Mohammed ya aiko.

Kirista Mahajjatan jihar Bauchi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG