Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin Amurka Zuwa Koriya Ta Arewa Zai Gana Da Jami'n Koriya Ta Kudu Laraban Nan


Wakilin Amurka namusamman zuwa Koriya ta Arewa Srephen Bosworth,yake magana da manema labarai da isarsa koriya ta kudu
Wakilin Amurka namusamman zuwa Koriya ta Arewa Srephen Bosworth,yake magana da manema labarai da isarsa koriya ta kudu

Ana kyautata cewa za su maganta ne akan sharudan da ya kamata gwamnatin Kuriya ta arewa ta cika kafin a sake tattaunawa da ita a kan raba ta da makaman nukiliya.

Manzon Amurka na musamman a Kuriya ta arewa Stephen Bosworth zai gana da shugaban hukumar makamashin nukiliyar kasar Kuriya ta kudu, Wi Sung-lac a yau laraba a birnin Seoul.

Ana kyautata cewa za su maganta ne akan sharudan da ya kamata gwamnatin Kuriya ta arewa ta cika kafin a sake tattaunawa da ita a kan raba ta da makaman nukiliya, sharudan sun hada da dakatar da shirye-shiryen ta na nukiliya da kuma barin jami’an binciken kasa da kasa su sake komawa kasar.

Da ya isa kasar Kuriya ta kudu a jiya talata, Bosworth ya yi kiran cewa tattaunawa da gaske gadan-gadan ne babban shirin da zai shawo kan kasar ta kwaminisanci.

Tattaunawar da kasashe shidda ke yi a kan raba Kuriya ta arewa da makaman nukiliya ta cije, amma a kwanan nan gwamnatin kasar Kuriya ta arewar ta nuna alamu, ta na da aniyar so a ci gaba da tattaunawar.

Bosworth ya yi wannan tafiya ce wadda za ta kai shi har kasashen China da Japan, a gabannin wani taron kolin da za a yi tsakanin shugaban Amurka Barack Obama da shugaban kasar China Hu Jintao a ranar 19 ga watan nan na janairu a nan birnin Washington, D.C, inda ake kyautata cewa kasar Kuriya ta arewa ce babban abun da za su tattauna a kai.

A jiya talata, shugaba Obama ya gana da ministan harakokin wajen kasar China, yang Jiechi wanda ya zo nan birnin Washington domin share fagen ziyarar da Mr.Hu zai kawo.

XS
SM
MD
LG