Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Gwada Wani Babban Makami


Wani makamin Koriya Ta Arewa
Wani makamin Koriya Ta Arewa

A wani al'amari mai nuna irin yadda Koriya Ta Arewa ke yin watsi da irin kashedin da duniya ke yin ma ta, kasar ta gwada wani dirkeken injin din harba makami ko kuma wata rokar 'yan sama jannati

Koriya Ta Arewa ta gwada wani katafaren injin din cilla roka daga kasa, a cewar kafar labaran gwamnatin kasar ta KCNA a yau dinna Lahadi.

Shugaban Koriya Ta Arewar Kim Jong Un ya ce an yi nasara a wannan gwajin, sannan ya "jaddada cewa kwanan nan duniya za ta ga irin gagarumar nasara mai kafa tarihi, wadda mu ka yi yau," a cewar kafar ta KCNA.

Wannan gwajin ya kunshi harba injin din rokar yayin da ya ke bisa wata marika a kasa, ba tare da harba wani makami mai linzami ba. An yi wannan izawar ce a tashar harba roka ta Tongchang-ri, daura da iyakar Koriya Ta Arewar da China, a cewar kafar ta KCNA, wadda ta ce Kim Jong Un ya je tashar da asuba, ya kafa tabaron hangen nesa sannan ya bayar da umurnin fara gwajin.

Tuni dai Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, wanda ke ziyarar aiki a karon farko a Nahiyar Asiya, tun bayan zamansa Sakataren, ya yi kiran da a bullo da wata sabuwar hanyar tinkarar karuwar barazanar nukiliya daga Koriya Ta Arewa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG