Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Kudu: Kotu Ta Yi Watsi Da Sammacin Kama Shugaban Kamfanin Samsung


Shugaban kamfanin Samsung Lee jae-yong
Shugaban kamfanin Samsung Lee jae-yong

Wata kotu a Koriya ta Kudu yau Alhamis tayi watsi da takardar sammacin kama shugaban kamfanin Samsung, a wani batun da zai shafi shari’ar tsige shugaba Park Geun-hye.

An tsare Jay Y. Lee mataimakin shugaban Samsung har tsawon sa’oi 14 a wata cibiyar tsare mutane, kafin kotun lardin tsakiyar Seoul ta yanke hukumci cewa, babu isassar shaida a daidai wannan lokacin da ta goyi bayan tuhumar da ake yi masa kan cin hanci da rashawa da kuma shaidar zur.

Alkalin da ya saurari karar ya fidda wata sanarwa da take cewa, bayan sake duban binciken da hanyar da aka gudanar da binciken, mawuyacin abu ne a tabbatar da dalilai da kuma hujjar kama shi a daidai wannan lokacin.

Ana zaton Lee, ya ba wani babban abokin shugaba Park mai suna Choi Soon-sil, cin hancin dollar miliyojn 36 domin neman taimakon shugaban kasar wajen samun amincewar gidauniyar fansho wajen hade wadansu kamfanoni biyu da suke mu’amala da kamfanin Samsung a shekarar 2015. An bada kudin ne a matsayin taimako don horar yar Choi da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu na boge.

XS
SM
MD
LG