Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Ta Kai Wani Hari Da Makamai Masu Guba a Iraqi.


Wasu da harin gubar da ISIS ta kai ta farwa suke dakon jinya a wani asibiti.
Wasu da harin gubar da ISIS ta kai ta farwa suke dakon jinya a wani asibiti.

Wata 'ar shekaru uku da haifuwa da mutu wasu daruruwa kuma sun jikkata.

A Iraqi, kungiyar ISIS ta kai hare hare biyu da makamai masu guba kusa da birnin kirkuk a arewwcin kasar Asabar din nan , wata yarinya 'yar shekaru 3 da haifuwa da mutu, wasu dari shida kuma sun jikkata, wasu daruruwa kuma sun tsere.

Jami'an tsaro, da ma'aikatan kiwon lafiya suka ce harin na ranar Asabar, ISIS ta auna wani karamin wuri ne da ake kira Taza, garin da kwanaki uku da suka wuce kungiyar ta kai hari da makamai masu guba data culla su da rokoki.

PM kasar Haider al-Abadi, yayi alwashin gwamnatinsa zata dauki fansa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau, shugaban kasar yace, 'yar shekaru uku da haifuwan ,mutuwarta ba zama a banza ba.

Ahalinda ake ciki kuma, rundunar mayakan sama na Turkiyya ta kaddamar da farmaki da jiragen yaki kan 'yan tawayen kurdawa a arewacin Iraqi ta kashe akalla mayakan sakai 67, kamar yadda rundunar tayi bayani yau Asabar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG