Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty International Ta La’anci Gwamnatin Gambia


amnesty international
amnesty international

Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta la’anci gwamnatin kasar Gambia saboda ficewarta daga kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC, abinda Amnesty ta kira babban kalubale ga miliyoyin mutanen da ake cin zarafinsu a fadin duniya.

Ayayid da take bada sanarwan ficewarta daga babban kotun ta birnin Hague shekaranjiya Talata ne, Gambia take zargin kotun da yin watsi da duban laifukan yaki da ake aikatawa a kasashen duniya daban-daban,.

Shawarar ficewar da Gambia ta dauka ta biyo bayan irin wannan mataki ne da Afrika ta Kudu da Burundi suka dauka na ficewa daga Kotun ta ICC.

To amma Darektan nazari da gangami na kungiyar Amnesty International a nahiyar Afrika Netsanet Belay ya fada a jiya Laraba cewa a maimakon kasashen Afrika su ci gaba da ficewa daga Kotun, yakamata su yi koyi da Botswana su yi aiki tare da kotun wajen warware batutuwan dake damunsu.

Belay yace ga yawancin mutane Afrika, ta hanyar wannan kotun ne kawai zasu samu adalci daga cin zarafi da aka dade ana musu.

Sai dai kuma Ministan yada labarai na Gambia Sheriff Bojan yace wannan Kotu duk da cewar ana kiranta da sunan ta kasa da kasa, a kashin gaskiya kotu ce da ba abinda tasa a gabanta illa muzgunawa mutanen da ba Turawa ba, musamman ‘yan kasashen Afrika.

Masu sukar lamairi ga wannan kotun, sunce kotun ta fi maida hankalinta kan kasashen Afrika ta yi watsi da laifukan yaki dake faruwa a wasu sassa na duniya. Har aka bada misalin cewa daga cikin shara’oi 10 da kotun tayi aiki a kansu izuwa yanzu, daya ne kawai ba wanda ya shafi kasashen Afrika ba.

XS
SM
MD
LG