Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Sabbin Hare-hare Nijar


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

A wani yunkurin da ya zama tamkar mayarda martani, kungiyar Boko Haram ta kai hari garin Diffa

Kungiyar Boko Haram daga Najeriya ta kaddamar sabbin hare hare a Nijar da kamaru jiya Litininin, a dai dai lokac inda shugaban kungiyar yayi alwashin galaba kan sojojin kasashe da suke fafatawa dasu.

Shaidun gani da ido sun ce 'yan binidga sun kai hari kan wani gidan fursina a kudu maso gabasshin Nijar a garin Diffa, amma sojojin Nijar sun fatattakesu. Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan yawan mutanen da harin ya rutsa dasu, ko kuma akwai kuma fursinoni da suka tsere.

Daga bisani an samu rahotani daga arewacin Kamaru dake cewa mayakan sakan sun kama wata motar safa da mutane akalla 18. Wani mazaunin wani gari da ake kira Koza ya gayawa kamfanin dillancin labaran Associted Press cewa mayakan sun tuka motar zuwa kan iyakar Najeriya.

A wani fefen vidiyo da aka saka a dandalin Youtube, an nuna shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yana ba'a ga rundunar sojojin yanki dubu bakwai da ake shirin girkewa, cewa ai sunyi kadan, domin mayakansa zasu karkashesu daya bayan daya.

Haka nan kuma yayi barazana ga shugaban Cadi Idris Deby, wanda sojojin kasarsa suka fafata da mayakan Boko Haram a Najeriya da Nijar da kuma Kamaru cikin makon jiya.

XS
SM
MD
LG