Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane a Kamaru


Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram

Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta kashe mutane bakwai cikin wadanda take cafke dasu a Kamaru.

Wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne daga Najeriya sun kashe wasu daga cikin fasinjojin dake cikin motar safar da suka kama a kasar Kamaru ranar Litinin din nan.

Wanda ya ga lamarin ya shaidawa Muryar Amurka cewa mayakan sun hallaka mutane 7 cikin 20 da suke rike dasu kana suka jefar da gawarwakinsu a arewacin kasar ta Kamaru dake kan iyaka da Najeriya.

Shetima Ahmadu shugaban wata makarantar gwamnati a yankin yace danuwansa dake tuka motar an samu gangar jikinsa babu hannaye da kafafu.

Ya kara da cewa mayakan sun saki mata tsoffi uku amma sun cigaba da rike mutane 10 da suka hada da ‘yan mata masu shekaru kimanin 11 zuwa 14.

Mai magana da yawun dakarun Kamaru Kanal Didier Badjeck da gwamnan yankin Mijinyawa Bakari sun tabbatar da jefar da gawarwakin amma sun ce suna jiran su san adadin wadanda aka rutsa dasu.

Kasar Kamaru na cikin kasashen Afirka uku da dakarunsu na fafatawa da kungiyar Boko Haram cikin ‘yan makonnin nan. Sauran kasashen su ne Nijar da Chadi.

Ko ranar Litinin din nan sai da sojojin Nijar suka dakile yunkurin da kungiyar Boko Haram tayi na kai hari akan wani gidan kaso a Diffa. Amma duk da haka sai da wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar da bom da ya hallaka mutane shida a Diffan.

XS
SM
MD
LG