Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Yi Mubaya'a Da ISIS


Imam Abubakar Shekau
Imam Abubakar Shekau

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sanar da yin mubaya’a da kungiyar ISIS, 'yan sa'oi bayan tashin bama - bamai da suka hallaka sama da mutane hamsin a jihar Borno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sanar da yin mubaya’a da kungiyar ISIS, yayin da a ke samun rahotannin tashin bama-bamai da suka hallaka sama da mutane hamsin a jihar Borno inda kungiyar Boko Haram ta ke da karfi.

Kungiyar da ke sa ido kan ayyukan ta’addanci mai suna SITE, ta ambaci ta bakin kungiyar Boko Haram jiya ta na cewa, “mu na mubaya’a da Kalifa” a wani sabon bidiyo da a ke kyautata zaton ya fito ne daga kungiyar mayakan Najeriya.

Kungiyar ISIS ta na iko da wadansu sassan Iraq da Syria kuma ta na kiran shugabanta Kahlifa.

Sanarwar ta biyo bayan wadansu hare-hare da a ka kai a Maiduguri babban birnin jihar Borno da ya yi sanadin rasuwar sama da mutane 55 kimanin 140 kuma su ka ji raunuka.

Wakilinmu Haruna Dauda Bi’u na da karin bayani dangane da hare-haren da a ka kai a jihar Borno.

Rahoton Hari a Maiduguri-2:00
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG