Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar PENE Da BWATIYE Ta Yi Kira A Gaggauta Tsige Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Adamawa


Kungiyar gamayyar kabilar Bachama da Bata ‘ Pene da Bwatiye’ ta yi kira ga sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya gaggauta tsige kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa Mohammed Ghazali saboda dalilai na sakaci da aiki da ya yi sanadin salwantar rayuka saba’in da biyu a kauyuka tara da ke kananan hukumomin Gerei da Demsa daga ranar ashirin da huda na watan junairun bana.

Kungiyar ta sanarwa taron manema labarai ta bakin shugabanta Yerima Hazron Fada da ta kira a cibiyar ‘yan jaridu ta Najeriya reshen jihar Adamawa lokacin da kungiyar ke maida martini ga kalaman kwamishinan ‘yan sanda na ranar biyu ga watannan inda yake cewa ba a sami asarar rai ko daya ba biyo bayan harin da fulani makiyaya suka kai kauyen Kodomun na karamar hukumar Demsa kwanaki uku a jere da ya yi sanadin mutuwar mutane ashirin da biyar.

Cikin jawabin da ya karantawa ‘yan jarida, shugaban kungiyar ya yi gargadin al’umarsa za su dauki matakan tsare rayukan jama’arsu da dukiyoyinsu matukar gwamnatin jihar Adamawa da jami’an tsarro basu dauki tsauraran matakai na tsaron lafiyarsu, dukiyoyi da sake tsugunar da mutane sama da dubu biyu da dari biyar da rikici sakanin Fulani makiyaya da manoma ya raba da muhallansu ba.

Wani Hon, Garba daya daga ciki magabatan kungiyar Pene Da Bwatiye da na yi hira da shi ‘yan mintoci bayan kamala taron ‘yan jaridu da kungiyar ta kira, ya ce bukatunsu sun hada da sake tsugunar da jama’arsu, kafa kotun sauraron keta hakkin bil’adama da kuma na sifeton janar na ‘yan sandan Najeriya ya tsige kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa saboda sakaci da rashin sanin makamar aiki.

Wakilinmu Sanusi Adamu na dauke da sauran rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG