Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Dillalan Man Fetur Zata Kawo Karshen Karancin Mna


Matatun man fetur
Matatun man fetur

Sabili da samun lasisin gina sabbin matatun mai a kasar, kungiyar dillalaln man fetur tace nan ba da dadewa ba zata kawo karshen karancin man da kasar ke fama da shi.

Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya ta samu lasisin gina sabbin matatun mai.

Sakataren kungiyar ta kasa Danladi Garba Fasali yace sun samu lasisi kuma sun samu filayen da zasu gina matatun a jihohin Bayelsa da Kogi. Tuni sun kira wasu kwararru daga kasashen waje har sun duba wuraren. Gwamnati ma ta yadda ta yi sassauci.

Maimakon gwamnati ta dinga ba masu shigo da tacaccan mai tallafi kamata yayi a ba wadanda zasu tace a cikin kasar tallafi wanda kuma gwamnati ta yadda da hakan. Idan aka kafa matatun za'a iya daukan akalla mutane miliyan daya aiki.

Za'a gina matatun da hadin gwiwar masu saka jari daga waje. 'Yan kasuwa daga Ingila sun taru sun hada hannu su zuba jarin dalar Amurka biliyan uku. Su kuma 'yan Najeriya da kungiyar dillalan man fetur zasu saka kashi 60 cikin dari na kudaden da ake bukata ko kuma dalar Amurka biliyan bakwai da miliyan dari biyar.

Sabili da karancin wutar lantarki a Najeriya matatun zasu tanadi nasu wutar da zasu yi anfani da ita.

Ga cikakken bayani na Medina Dauda.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG