Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Fulanin Nijar Ta Shirya Taron Makiya da Manoman Nijar da Najeriya


Kasuwar Shanu tsakanin Najeriya da Nijar
Kasuwar Shanu tsakanin Najeriya da Nijar

Domin samun zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma da kuma takwarorinsu na tarayyar Najeriya ya sa kungiyar makiyaya ta jamhuriyar Nija ta shirya wasu tarurruka biyu a birnin Konni dake kan iyaka da Najeriya da kuma Doso

Tarukan biyu sun samu mahalarta daga kasashen biyu saboda samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin Fulani makiyaya da manoman kasashen biyu.

Tarukan sun zama wajibi domin makiyaya su kan tsallaka iyakokin kasashen. Fulanin Nijar na shiga Najeriya haka ma na Najeriya na shiga kasar ta Nijar banda kasuwannin dabbobi dake tsakaninsu.

Malam Ahmadu Halilu shugaban kungiyar Fulanin Nijar yace sun kira kungiyoyin manoma da makiyaya domin su yi nazari akan hanyoyin da zasu zauna lafiya. Yace kowace sana'a na bukatar zaman lafiya. Yadda mutane suke da hanyoyin bi haka ma yakamata a kebewa dabbobi hanyoyin da zasu bi.

A nasa bangaren Malam Ali Muhazari shugaban fulani daga tarayyar Najeriya yace tarukan zasu bada damar yadda za'a shimfida zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a kasashen biyu.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG