Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadin Kan Afirka Ta Janye Dakatar Da Mali Da Tayi


Sojoji suna gadi a tashar jirgin sama bayan juyin mulki a Mali
Sojoji suna gadi a tashar jirgin sama bayan juyin mulki a Mali
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage dokar dakatar da kasar Mali daga cikin kungiyar, a dai dai lokacinda take shirin tura dakaru kasar dake yammacin Afirka.

Jami’an kungiyar suka ce yanzu Mali tana iya shiga a dama da ita cikin duka harkokin kungiyar.

A cikin watan Maris ne Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali bayan da wani gungun sojojin kasar suka ayyana juyin mulki, mako biyu kamin a yi zaben shugaban kasa.

Mayakan sakai da ake zargin suna da alaka da al-Qaida sun kama arewacin Mali.
har sun fara aiwatar da tsarin shari’a mai tsanani da suka hada da aiwatarda hukuncin kisa da bulala a bainar jama’a. Gwamnatin wucin gadi ta Mali ta nemi a tallafa mata wajen ganin an tusa keyarsu.

Tarayyar Afirka tana shirin tura sojoji Mali tareda taimakon Majalisar Dinkin Duniya, da tarayyar turai, da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka, watau ECOWAS.
XS
SM
MD
LG