Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Boko Haram Ta Kai Hari A Kasar Cadi.


Sojojin Cadi
Sojojin Cadi

A karon farko, kungiyar Boko Haram ta kai hari kan wani kauye a Cadi, a zaman wani bangare na fadada tada kayar bayar da yanzu ta shafi kasashe hudu.

Jami'an kasar Cadi suka ce an kashe akalla mutane 12 ciki harda dagacin yankin, a tarzomar da 'yan bindigar suka kai kan kauyen da ake kira Ngouboua. Suka ce 'yan bindigar sun shiga kasar ne ta wajen amfani da jiragen ruwa suka ratsa tafkin cadi, a safiyar jiya jumma'a.
Mayakan sakan sun cunna wuta kan wani bangaren kauyen, kamin sojojin kasar su koresu.
Sojojin Cadi sun ce dakarunsu sun kasa bin sawun 'yan binidgar saboda basu da jiragen ruwa, amma jiragen yaki masu saukar ungulu sun kai farmaki ta kan ruwan tafkin cadi, suka lalata jiragen ruwan 'yan binidgar da suke kokarin tserewa.
Gwamnan yankin tafkin cadi, Bayana Kossinger, yace cikin wadanda aka kashe a fadan da aka gwabza, harda sojojin kasar biyu, farar hula biyar, damayakan sakai biyar, daga cikin 'yan binidgar.

Tuni dama kauyen na Ngouboua, ya zama sansanin wasu 'yan gudun hijira daga Najeriya su fiyeda dubu biyu,wadanda suke kokarin kaucewa rikicin na Boko Haram. Shugaban kula da sansanin 'yan gudun hijira Idris Peve, yace babu daya daga cikin 'yan gudun hijirar da harin na jiya Jumma'a ya rutsa dasu.
A baya, kungiyar 'yan binidgar ta kai munanan hare hare kan wasu garuruwa a kasashen kamaru da Nijar.
Kamaru da Nijar tareda cadin, a baya bayan suka hada karfi na kafa rundunar yanki wacce zata yaki masu tsatstsauran ra'ayin addinin.
Amurka tayi Allah wadai da harin da Boko Haram ta kai, kuma ta mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda harin ya rutsa dasu, da kuma wadanda tashe tashen hankulan suka raba su da muhallansu.

XS
SM
MD
LG