Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Da Gwamnatin Najeriya


Kungiyar Kwadago ta Najeriya tana ci gaba da bayyana rashin amincewarta da janye tallafin mai da gwamnati ta yi a kasafin kudin bana
Kungiyar Kwadago ta Najeriya tana ci gaba da bayyana rashin amincewarta da janye tallafin mai da gwamnati ta yi a kasafin kudin bana

Labarin da ya fito a jaridar Guardian dake nuna gwamnatin Najeriya zata zanta da kungiyar Kwadago don amincewa da mafi karancin albashi Naira Dubu 45 da hakan kuma zai kai ga rage ma’aikata ya tsaya nan kawai, babu wani karin bayani daga wata majiya mai tushe.

Hakan ma na alakanta biyawa kwadagon bukata don kawar da batun yajin aiki daga karewar wa’adin na gobe Laraba, na neman dawo da litar Mai Naira 86. Ba alamar gwamnati zata ja da baya haka nan itama kungiyar Kwadagon dake samun gwalewa daga sassan ma’aikata da talakawa dake cewa ba zasu marawa yajin aikin baya ba.

A baya dai ministan Kwadago Chris Ngige, ya jaddada gwamnati zata samar da karin ayyukanyi maimakon rade radin rage ma’aikata. Haka kuma yayi karin haske kan tanadin da kasafin kudi yayiwa ma’aikata.

Shi kuma shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, Ibrahim Khalil, ya nuna ba lalle bane karin albshin ne damuwar ba, amma yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabi.

Alamu na nuna matakin kungiyar Kwadagon kan iya samun tasiri ko matsakaicin tasiri a wasu yankuna da jam’iyyun adawa ke da tagomashi da kuma tsakanin talakawan dake ganin ba ranar karewar talauci a Najeriya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG