Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Malaman Jami'a Da Kungiyar Kwadago Sun Yi Taro


Masu zang-zanga
Masu zang-zanga

Yayin da knugiyar malaman jami'a na cigaba da yayin aiki da ta shiga cikin 'yan watanni da suka gabata sai gashi ta yi taro da kungiyar kwadago.

Daruruwan tsoffin ma'aikata da yan kwadago da kungiyar malaman jami'a suka yi taro a babban zauren taro mai tarihi dake birnin Ibadan da ake kira Mapo Hall jiya Alhamis.

Makasudin taron shi ne don tattaunawa game da yajin aikin da malaman jami'o'i ke cigaba da yi da kuma fadakar da jama'a. Tsohon ministan albarkatun kasa na Nijeriya Farfasa Tom David West na daya daga cikin waddanda suka halarci taron. Ya ce yakamata gwamnatin Nijeriya ta bada ilimin jami'a kyauta. Ya ce ya kamata ta yi koyi da kasashen Ghana da Uganda da Afirka Ta Kudu wadanda na bada kashi ashirin da biyar na kasafin kudadensu ga harkokin ilimi.

Shugaban kungiyar malaman jami'a reshen Ibadan Dr Olusegun Ajiboye ya ce sun shirya taron ne domin su ilimantar da jama'a game da abubuwan dake faruwa dalilin yajin aikin. Ya ce baiwa sashen ilimi isasshen kudi yakamata ya zama abun da ya damu kowa da kowa. Shi kuma shugaban kungiyar kwadago ta jihar Oyo ya ce ya lura da damuwar kungiyar malaman jami'a da rashin isasshen kudi da wahalar da dalibansu ke sha. Shugaban wata kungiyar ma'aikata Kwamred Erubami ya ce yakamata gwamnati ta fahimci cewa samarma mutane ilimi zai bunkasasu.

Hassan Umaru Tambuwal nada rahoto daga Ibadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG